Ofishin zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin, da ofishin kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar sun yi maraba da halartar manema labaru na cikin kasar Sin da na waje, tare da fatan za su gabatar da tambayoyi a yayin manyan tarukan da kasar za ta shirya.
Za dai a bude taron shekara shekara na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin, da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, a ranar 5 da ranar 3 ga watan Maris na wannan shekara a nan birnin Beijing. (Lami)