in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hasashe kan tattalin arzikin Afrika ta Kudu yayi kasa a shekarar 2016
2016-01-29 09:43:47 cri
Ana saran karuwar tattalin arzikin Afrika ta Kudu zai iya raguwa zuwa kashi 0.9 cikin 100 a shekarar 2016, idan aka kwatanta da hasashen da aka yi a da wanda ya nuna tattalin arzikin kasar zai iya karu da kashi 1.5 a bana, kamar yadda babban bankin kasar ya sanar a Alhamis din nan.

Babban bankin na Afrika ta Kudu ya fada cewar ana saran tattalin arziki kasar zai karu ne bisa hasashen samun bunkasuwa a kayayyakin da ake samarwa na cikin gida, inda akayi hasashen karuwar sa zuwa kashi 1 da digo 6 a shekarar 2017, kasa da yadda akayi hasashe da farko na samun karuwar kashi 2 da digo 1 cikin 100.

Babban bankin kasar ya fada bayan kammala zaman kwamitin al'amurran kudin kasar MPC cewar, bisa hasashen da aka yi, karuwar tattalin arzikin kasar a shekarar 2015 ta kai kashi 1 da digo 3 cikin 100.

Yanzu dai hasashen da bankin yayi ya gamu da nakasu, na samun karuwar kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje da kashi 1.9 ya koma kashi 1.5 a 2016, sannan daga yiwuwar karuwar kashi 2.1 ya koma kashi 1.6 a 2017. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China