in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan cinikayyar dake tsakanin Sin da Afrika ta Kudu ya kai dalar Amurka biliyan 46
2016-01-08 11:38:18 cri
Bisa bayanan da wakilinmu ya samu a wajen taron masana'antun Sinawa da aka shirya a birnin Pretoria da ke Afrika ta Kudu, an ce. Yawan cinikayya tsakanin Sin da Afrika ta Kudu ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 46 a shekarar 2015, kuma kasar Sin za ta zame ma Afirka ta Kudu babbar abokiyar cinikayya, da kasuwar fitar da kayayyaki da wurin shigar da kayayyaki mafi girma har shekaru 7 a jere.

Jakadan Sin a kasar Afrika ta Kudu Tian Xuejun ya ce, shekarar 2015 ta kasance mai ma'ana musamman ga dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ta Kudu, da kuma tsakanin Sin da sauran kasashen Afrika, sabo da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu ta samu babban ci gaba. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci Afrika ta Kudu da halartar taron kolin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kuma ya nuna alkiblar raya hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afrika ta Kudu, da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika, kuma amincewar juna a fannin siyasa da manyan dabarun raya kasashen biyu ya kai matsayin koli da ba a taba ganin irinsa ba, kuma akwai makoma mai haske game da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Bisa sabuwar kididdigar da karamin ofishin jakadancin Sin da ke Afrika ta Kudu mai kula da batun tattalin arziki da cinikayya ya yi, an ce, yawan masana'antun Sin da ke Afrika ta Kudu ya kai 140, kuma yawan jarin da aka zuba a Afrika ta Kudu ya kai dalar Amurka biliyan 13, sannan akwai ma'aikata Sinawa kimanin 1300 dake aiki a can, kana, an dauki ma'aikata 'yan kasar Afirka ta Kudu sama da dubu 20, kuma al'amarin ya sa kaimi ga raya tattalin arziki da cinikayya da samar da guraben aikin yi a wurin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China