in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana da tabbacin za'a cimma matsaya a karshen taron sauyin yanayai Asabar din nan
2015-12-12 17:01:05 cri
Kasar Sin ta ce tana da tabbacin cewa za'a cimma matsaya a karshen taron sauyin yanayi a ranar Asabar din nan a birnin Paris.

Kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen Sin Liu Zhenmin ya fadi a ranar Jumma'an nan, ya ce tawagar kasar suna ta aiki tukuru a cikin makonnin da suka gabata da sauran masu ruwa da tsaki da duk abokan hadin gwiwwa wajen ganin an cimma ma matsayan karshe a taron.

A bayanin da ya yi ma manema labarai, ya ce yana da tabbacin cewa a yau Asabar din nan za'a cimma matsaya mai kyau.

Mr Liu ya ce batun banbance banbance yana kan gaba a cikin damuwar da Sin take da shi a game da matsayar da za'a cimmawa na Paris. Ya ce nace ma bin ka'idpjin da aka amince da su game da banbancin da ya zo daya da kuma nauyin dake kan kowa.

A cewar mr Liu, kasashe maso tasowa sun bukaci kasashen da suka ci gaba da su cika alkawarinsu wajen rage fitar da hayaki mai gurbata yanayi, sannan kuma su taimaka ma kasashe maso tasowa magance nasu matsalar sauyin yanayin. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China