in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata a tattauna batutuwan siyasa a gun taron APEC ba, a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin
2015-11-11 21:03:24 cri

Kakakin ma'aikatan harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, taron APEC dandali ne mai muhimmanci da ake tattauna harkokin tattalin arziki na yankin Asiya da Pacific, amma ba wuri ne na yin shawarwarin harkokin siyasa ba,don haka bai kamata a tattauna batutuwan siyasa a gun taron ba.

Hong Lei ya bayyana hakan ne yayin da yak e mayar da martani ga kalaman da kakakin majalisar gudanarwar kasar Amurka ya yi cewa, watakila a tattauna batun tekun kudancin kasar Sin a gun taron na APEC. Hong Lei ya kara da cewa, kasashe membobin kungiyar APEC ba za su cusa batutuwan da suka shafi siyasa cikin abubuwan da za su tattauna dandanlin ba, hakan ya sa, wannan ya sa har yanzu ake ci gaba da yin dandalin tattaunawar na APEC.

Ya ce sun fahimci cewa, kasar Philippines, mai masaukin bakin taron na APEC ba za ta yarda a tattauna batutuwan siyasa da tsaro ba. Don haka suna fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su tabbatar da ingancin taron APEC domin inganta bunkasuwar tattalin arziki da hadin gwiwa a shiyyar, ta yadda za a gudanar da taron ciki nasara tare da ingiza bunkasuwa da hadin gwiwa a tsakanin kasashe daban daban.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China