in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban kasar Sin a Birtaniya za ta bude sabon shafin dangantakar kasashen biyu
2015-10-16 13:40:11 cri

A jiya ne jakadan Sin dake Birtaniya Mista Liu Xiaoming ya kira wani taron manema labaru a birnin London, don yin karin haske kan ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai wa kasar Birtaniya. A cewarsa, ziyarar a wannan karo na da ma'ana sosai.

Mutane kimanin 70 ne suka halarci taron manema labarun da aka kira , ciki hadda wakilan BBC, gidan telibiji na CNN da ke Amurka, kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa AFP da sauran manyan kamfanonin dillancin labarai na kasar Birtaniya gami da 'yan jaridar kasar Sin dake Birtaniya.

Jakada Liu ya yi bayanin cewa, wannan shekara ta kasance shekara ta 11 bayan da aka kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu wato Sin da Birtaniya. Saboda haka firaministan kasar Birtaniya Mista David Cameron yana daukar wannan shekara a matsayin shekara mai muhimmanci ta kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2. Ta la'akarin da muhimmancin lokacin da ake ciki,a cewar jakadan Sin, shugaba Xi na kasar Sin ya zabi wani lokaci mai dacewa ne domin ya yi ziyara a kasar Birtaniya. Mista Liu ya ce:

"Shugabannin kasashen biyu za su tsara sabon tsari kan dangantakar da ke tsakanin kasashen 2, tare da bullo da sabbin muradu da shirye-shirye. Hakan ya sa, ziyarar ta wannan karo za ta zama matakin dake hada yanayin da ake ciki a baya da kuma na nan gaba, kana za ta taimaka wajen karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin 2 nan gaba."

Ban da wannan kuma, Mista Liu ya ce, Birtaniya za ta shirya gaggarumin bikin al'adun gargajiya don maraba da shugaba Xi Jinping. Yayin bikin ana sa ran harba bindigogi sau 103 domin maraba da babban bakon, inda mambobin masarautar Birtaniya na zuriyoyi uku za su halarci bikin tarbar Shugaba Xi da mai dakinsa Madam Peng Liyuan.

Yayin ziyarar tasa, Mista Xi zai yi jawabi a majalisar dokokin kasar Birtaniya, baya ga ganawa da manyan shugabannin kasar, Mista Xi zai halarci bukukuwa da dama da za a yi a birnin London tare da kai ziyara birnin Manchester, inda firaministan Cameron zai yi masa rakiya.

Dadin dadawa, Mista Cameron da mai dakinsa Samantha za su gayyaci Mista Xi da mai dakinsa don su ziyarci gidansu a Chequers dake wajen birnin London. A nata bangare, kasar Sin ta dora matukar muhimmanci kan ziyarar ta Mista Xi a wannan karo, saboda a wannan karo shugaba Xi zai yi ziyara zuwa kasar Birtaniya kawai, ba kamar yadda ya saba da yinsa a baya inda ya kan ziyarci wasu kasashe daya bayan daya a karo guda.

Kazalika, a wannan rana, jakada Liu ya bayyanawa manema labaru game da ziyarar da shugaba Xi zai kai wasu shahararrun jami'un kasar. Ya ce

"Shugaba Xi zai kai ziyara a cibiyar nazarin fasahar mutum-mutumin inji da nazarin kwayoyin halittu dake jami'ar Imperial College ta Birtaniya, zai kuma gana da wasu masana a jami'ar Mancherster wadanda suka samu lambar yabo ta Nobel."

Yayin da Mista Liu yake bayani kan hadin gwiwar da kasashen biyu za su yi a fannin kwallon kafa, ya ce

"Birtaniya ta yi suna sosai a fannin kwallon kafa, yayin da Sin kuma ta ke kokarin daga matsayinta ta fuskar wasan kwallon kafa, don haka bangarorin biyu na da makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a wannan fanni."

An ba da labarin cewa, kafofin yada labaru daban-daban na kasar Birtaniya na mai da hankali sosai kan ziyarar da shugaban Xi zai kai a kasar ta Birtaniya a wannan karo. Jakada Liu shi ma ya zanta da wasu manyan kamfanonin dillancin labarai na kasar Birtaniya kan wannan batu, ciki hadda BBC, jaridar Financial Times da dai sauransu, inya ya yi karin haske kan ziyarar Xi Jinping a wannan karo, da kuma yanayin da kasashen biyu suke ciki ta fuskar dangantaka da hadin gwiwar da kasashen biyu suke yi a fannin ciniki, da yanayin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da sauran muhimman batutuwan da ke shafar bangarorin biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China