A tsawon wadannan kwanaki uku, tutocin kasar za su kasancewa zuwa rabin sanda a dukkan fadin kasarta Benin, kuma za a gudanar da salloli da adu'o'i a cikin masallatan mabiya addinin Musulunci domin nuna girmamawa ga mamatan. A cewar wata majiya ta kusa da sakataren kwamitin shirya hajjin shekarar 2015 na kasar Benin, mahajjatan Benin kusan goma ake tsammanin sun mutu, yayin da kuma wasu kusan satin aka rasa duriyarsu, daga cikin kimanin 'yan kasar Benin dubu hudu dake aikin hajjin shekara ta 2015 a kasar Saudiyya. (Maman Ada)




