in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Sin za su shirya faretin tunawa da cika shekaru 70 da kawo karshen harin Japanawa
2015-08-24 13:43:39 cri

Yayin da kwanaki 9 suka rage kafin a kaddamar da faretin murnar tunawa da cika shekaru 70 da samun nasara kan mayakan Japan da kuma yaki da masu ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya, sassa daban daban na Sin da na waje na dora matukar muhimmanci kan shirye-shiryen da ake game da wannan fareti.

Bayanai daga Wang Shun, mataimakin shugaban ofishin da ke kula da bikin faretin kuma mataimakin hafsan hafsoshin bataliyar sojojin yankin Beijing, na cewa, za a tsara faretin cikin rukunoni 50 da suka kunshi sojoji dubu 12, gami da muhimman na'urorin yaki na soja, wadanda kasar Sin ta kera da kanta, kana wannan shi ne karon farko da za a gabatar da kashi 84 cikin dari na wadannan na'urori a bainar jama'a. Ya zuwa yanzu an shiga mataki na karshe mai muhimmanci na gwajin wannan fareti.

Mataimakin shugaban ofishin da ke kula da bikin faretin kuma mataimakin hafsan hafsoshin bataliyar sojojin yankin soji na Beijing Wang Shun, ya bayyana cewa, za a shirya faretin ne cikin rukunoni 50, gami da muhimman na'urorin yaki na soja. Bugu da kari, za su gudanar da faretin ne bisa tsarin ayyukan da suke gudanarwa a fagen daga. Wang Shun yana mai cewa,

"A wannan karo, za a yi faretin bisa rukunoni 50, wadanda suka hada da rukunoni biyu na tsoffin sojoji da suka fafata a yakin kin harin Japanawa, da rukunoni 11 na sojoji da ke tafiya a kasa, da rukunoni 27 na na'urorin soja, da rukunoni 10 na jiragen saman yaki. Ban da wannan kuma, an tanadi kungiyar badujala da 'yan amshin. Sama da sojojin dubu 10 ake sa ran za su shiga faretin, wadanda suka fito daga manyan bataliyoyin sojin kasa guda 7, da sojin ruwa, da na sama, da sojojin da ke sarrafa makamai masu linzami, da 'yan sandan kwantar da tarzoma da dai sauransu. Bugu da kari, za a nuna daruruwan na'urorin soja, da jiragen saman yaki nau'o'i daban daban fiye da 100, kuma galibinsu sabbin muhimman na'urorin yaki ne, wadda kasar Sin ta kera da kanta. Kuma yawancin na'urorin da za a baje a lokacin wannan fareti,shi ne karon farko na bayyanarsu a bainar jama'a. Haka zakila, rukunonin soja daga kasashe fiye da 10 ne za su halarci wannan bikin fareti bisa gayyatar da kasar Sin ta yi musu."

A halin yanzu, an shiga muhimmin matakin karshe na gwaji. Wang Shun ya bayyana cewa, ana fatan kwalliya za ta biya kudin sabilu sakamakon horon da aka baiwa rukunonin sojojin daban daban. Wang ya kara da cewa,

"Yanzu haka rukunonin sojin da ke maci suna iya tsayawa cik har na tsawon sa'o'i biyu ba tare da son motsa ba. Haka zikila, suna iya tafiya cikin layi a jere har na tsawon mita 1000,suna jefa kafa a jere har na tsawon mita 200. Game da rukunonin na'urorin soja, yadda rukunonin ke wuce wa ba ya zarce dakika 0.3."

Bugu da kari, Wang Shun ya fayyace cewa, akwai abubuwa hudu da za a nuna a karon farko a cikin wannan fareti. Ya ce,

"Wannan shi ne karon farko da tsoffin sojojin da suka shiga yakin kin harin Japanawa za su shiga wannan fareti, lamarin da ya sheda muhimmiyar ma'anar tarihi na wannan bikin tunawa. Kana wannan ne karo na farko da muka gayyaci sojojin ketare domin shiga wannan faretin, wanda ya sheda nasarar da aka samu a fannin yaki da masu nuna ra'ayin karfin tuwo a fadin duniya. Har ila shi ne karon farko,da sojojin za su gabatar da fareti bisa tsarin ayyukan da suke gudanarwa a fagen daga, wanda ya sheda hadin gwiwar da za a yi koda yaki ya barke a nan gaba. Bugu da kari, wannan shi ne karon farko da masu mukamin janar na rukunonin soji za su shiga wannan fareti, wanda ya sheda muhimmancin kasancewar masu manyan mukamai a fagen yaki."

An fara gwajin faretin ne tun daga daren ran 22 ga wata zuwa tsakiyar ranar 23 ga wata a filin Tian Anmen da titin Chang Anjie don tabbatar da cewa, wannan muhimmin biki ya gudana kamar yadda aka tsara,.

Bayanai na nuna cewa, dukkan rukunonin soji sun shiga gwajin faretin, wanda ya kunshi sojoji daga kasashe fiye da 10 ciki hadda Rasha, Kazakhstan, Mongolia da sauransu, da kuma sojojin kasar Sin fiye da dubu 10, na'urorin sojin kasar sama da 500, jiragen saman yaki kimanin 200. Ban da wannan kuma, rukunin kiyaye tutar kasa, kungiyar 'yan badujala, kungiyar 'yan amshi, rukunin harba igwa don nuna girmamawa su ma sun halarci faretin. Dadin dadawa, jama'a kimanin dubu 35 ne suka kalli wannan biki.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China