in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gabatar da jawabi a yayin bikin rufe taron koli na masana'antu da cinikayya na Sin da Faransa
2015-07-03 14:12:16 cri

"Yayin muka siffanta dangantakar tsakanin Sin da Faransa tamkar wani babban jirgin sama, to, masana'antun kasashen biyu suna kasancewa tamkar injuna biyu na wannan babban jirgin ne. Muna fatan ba injuna biyu kawai za ku zama ba, ya kamata ku zama jirgi mai daukar injuna hudu. Sakamakon haka, za ku iya daukar fatan jama'ar kasashen Sin da Faransa zuwa wata kyakkyawar makoma."

A jawabin da Mr. Manuel Valls, firaministan kasar Faransa ya gabatar, ya taya murna da ziyarar Mr. Li Keqiang ya kawo wa Faransa da kulla dimbin yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, har ma ya nuna yabo ga burin da kasar Sin take son cimmawa kafin shekarar 2030 wajen tinkarar sauyin yanayin duniya da gwamnatin kasar Sin ta fitar a ran 30 ga watan Yuni. Game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, Mr. Valls ya bayyana cewa, "Ba ma kawai muna murnar dangantakar diplomasiyya da ta shafe rabin karni tana bunkasa tsakanin kasashen biyu ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne a cikin shekara daya ko fiye da ta gabata, shugabanni da gwamnatoci na kasashen biyu sun kawo wa juna ziyarce-ziyarce, inda suka bayyana wa sauran kasashen duniya hulda mai inganci kwarai dake tsakaninsu. Kasashen biyu suna da hangen nesa game da matsaloli da kalubaloli da ya kamata a fuskanta wajen bunkasa tattalin arziki a nan gaba. A lokacin da kasashenmu biyu ke kokarin tinkararsu cikin hadin gwiwa, tabbas ne daukacin duniya za ta samu makoma mai kyau."

Bayan taron, mahalarta taron sun nazarci jawaban da firaministocin biyu suka gabatar bi da bi. Mr. Christophe Nicot, manajan diraktan wani kamfanin kasar Faransa ya bayyana cewa, "Wannan taron kolin ya burge ni sosai. A cikin jawabin da firaministan kasar Sin ya gabatar, na ga yana murna sosai ga sakamakon da aka samu a yayin wannan ziyarar da ya kawo Faransa. Za mu yi kokarinmu wajen taimakawa masana'antun kasar Sin ta yadda za su tafiyar da harkokinsu da takwarorinsu na Faransa."

A jiya Alhamis ne kuma, kamfanin Huawei na kasar Sin da wani kamfanin kasar Faransa suka kulla wata yarjejeniyar yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Mr. Song Kai, babban direktan kamfanin Huawei reshen kasar Faransa ya bayyana cewa, "Firaministocin kasashen biyu sun bayyana wata kyakkyawar makoma a tsakanin kasashen biyu kan yadda za su kara yin hadin gwiwa a fannonin fasahohin zamani da makamashin nukiliya da zirga-zirgar jiragen sama da harkokin kudi da sha'anin noma da dai sauransu. Sannan za mu yi hadin gwiwa wajen nazarta sabbin fasahohin zamani tare, sannan mu yi amfani da su a kasuwannin bangare na uku, kamar a kasashen Brazil, Najeriya, Kongo, Indiya, inda darajar kwangilolin da kamfaninmu da kamfanin Alstom na kasar Faransa suka samu ta kai kusan dalar Amurka miliyan 20. Tabbas za mu yi kokarin yin haka." (Sanusi Chen)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China