Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana cewa mataimakiyar direkta a hukumar kayyade iyali da kiwon lafiya ta kasar Sin Madam Cui Li, za ta kasance wakiliyar musamman ta kasar Sin, wadda za ta halarci bikin murnar cika shekaru 40 da samun 'yancin kai a Cape Verde, bikin da za a gudanar a ranar 5 ga watan nan na Yuli. (Amina)