Tolentino ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi alkawarin raya tattalin arziki na nahiyar Afirka da sa kaimi ga bunkasa harkokin dan Adam, ana iya ganin babban ci gaban da aka samu a kasar Cape Verde a wannan fanni. Ya ce, an kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasarsa ta Cape Verde da kasar Sin tun daga lokacin da Cape Verde ta samu 'yancin kai a shekarar 1975. A cikin shekaru 20 da suka gabata, an zurfafa yin mu'amala a tsakanin kasashen biyu a fannonin ala'du da tsaron kasa da sauransu. A halin yanzu, yawan Sinawa dake kasar Cape Verde yana karuwa, yawancinsu matasa ne ko masu kafa kamfanoni, wadanda suka ba da gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Cape Verde. (Zainab)