A yanzu haka, yawan ribar da aka samu wajen dauraya zinariya ya ragu sosai. Gwamnatin Sin ta hana da a haka ma'adinai a yankin tsaunukan Qilianshan domin kiyaye muhalli a can. Amma a sa'i daya kuma, gwamnatin ta kara nuna goyon baya ga sana'ar aikin gona da kiwon dabbobi ba tare da gurbata muhalli ba. Mr. Ma ya samu sabon zarafin gudanar da kasuwanci, ya sake fara kiwon tumaki da saniya kamar yadda babansa ya yi a lokacin da. Ya ce,"A lokacin da nake karatu a makarantar firamare, babana ya tattara tumaki a garinmu don sayar da su zuwa jihar Ningxia, ya kan samu riba mai kyau. A shekarar 2007 da 2008, yawan tumaki da saniya da muke da su ya kai kimanin dari biyu. Daga bisani, bayan da na kafa kamfanina, yawan tumaki da na sayar a kowace shekara ya kai fiye da dubu 10, kuma yawan saniya da ya sayar ya kai fiye da dubu 4."
A shekarun baya, gwamnatin birnin Zhangye ta tsara wasu manufofi inda ta kalubalanci manoma da su dauke tumakai daga filin ciyayin dake kusa da tsunukan Qilianshan zuwa wuraren kiwon dabbobi da aka kebe, domin kiyaye muhalli na filin ciyayi, kuma ta tsara shirin kiwon saniya miliyan daya da shimfida filin ciyayi da fadinsa ya kai hectare dubu 70, domin raya sana'ar kiwon dabbobi da tattalin arziki maras gurbata muhalli. Ma Liming ya yi amfani da wannan zarafi, ya kafa kamfanin kayayyakin noma da dabbobi na Jinlihe a shekarar 2011 a birnin Zhangye, kamfaninsa na kula da saniya dubu 8 da tumaki dubu 10, kuma ya samu kudin taimako RMB Yuan dubu 400 daga gwamnatin birnin. A shekaru biyu da suka gabata, Mr. Ma ya fara shuka ciyayi a filin da fadinsa ya kai hectare 33 domin ciyar da dabbobi.
Birnin Zhangye yana da yanayi mai kyau, wanda ya dace da shuka kayan lambu sosai. A shekarar 2014, yawan kudin da aka samu wajen shuka kayan lambu a birnin ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 2.8. Ban da haka kuma, an tsara shirin bunkasa sana'ar kayan lambu na birnin Zhangye dake kan hanyar siliki, inda aka sa ran za a habaka fadin gonakin shuka kayayyakin lambu masu inganci da zai kai hectare kimanin dubu 70 a cikin shekaru biyar masu zuwa. Sabo da haka, Mr. Ma ya ga kyakkyawar makomar shuka kayayyakin lambu, ya yanke shawarar fara yin wannan aiki a nan gaba.
An gabatar da cewa, Ma Liming ya kulla kwangila tare da wani kamfanin sayar da na'urori dake lardin Shandong dake gabashin kasar Sin domin kafa sansanin kayayyakin lambu, inda kuma zai sayi na'urori da kuma nemi masu fasaha zuwa kamfaninsa domin shuka kayayyakin lambu masu inganci.(Lami)