150807-ziyarar-maryam-a-lardin-Gansu-2-lubabatu.m4a
|
"Na kan isa masana'anta a kowace rana da karfe 7 na safe domin ba da ayyuka ga ma'aikata, daga bisani, na tafi garken tumaki da rumfar saniya domin duba lafiyarsu, na kan sha aiki a duk rana har na gaji. Musamman ma a shekarar 2007 da 2008, kamfaninmu ya sha wahala sosai. Shugabana ya cimma nasara kamar haka, sabo da yana da basira."
Mr. Ma Liming shi ne shugaban wannan kamfanin kiwon saniya da tumaki, wanda Bai Guishan ya ce yana da basira, kuma shi ne wani musulmin da ya yi girma a wani kauyen yankin Ganzhou na birnin Zhang Ye, ya kula da wannan kamfani tare da 'dan uwansa a yankin aikin gona da kiwon dabbobi na Bajitan na unguwar Ganzhou, yawan saniya dake cikin kamfaninsu ya kai dubu 4 ko fiye, kuma yawan tumakinsu ya kai dubu 10 ko fiye, yawan jarin kamfaninsu ya kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 42. Ma Liming ya nada Bai Guishan ya zama manajan kamfaninsa, sabo da yana da fasaha, kuma ya sauke nauyin da aka dora masa. A yayin da yake magana kan aikinsa, Mr. Ma ya yi imani da cewa, "Ina da babbar niyyar cimma nasarar aikina, kuma zan yi iyakacin kokarin cimma wannan buri. Ina da shirin kara yawan dabbobin da muke kulawa. Na kan duba tumaki da saniya a rumfuna a kowace rana, ban da kwanakin da na tafi waje."
Mr. Ma ya kara da cewa, shi wani musulmi ne, shi ya sa, ya fi dacewa da gudanar da cinikayyar tumaki da saniya na halal. Yanzu haka, yana neman samun takardar izni na mahauci, domin kafa tambarin kamfaninsa.
Ana ganin cewa, Ma Liming ya samu babbar nasara wajen aiki. Amma Mr. Ma ya gaya mana cewa, ya sha wahalhalu sosai a yayin da ya fara aiki ba da dadewa ba, ya ce,"A lokacin farko, na yi ayyuka iri iri da dama, na taba sayar da na'urori da gina gine-gine da kuma dauraya zinariya a kudacin lardin Gansu."