in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da kungiyoyin mayakan dake amfani da yara
2015-06-19 10:34:11 cri

A jiya ne kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri da ke yin kakkausar suka ga kungiyoyin dakarun dake musayar wuta da amfani da yara a wajen yaki da kisa har ma da yin garkuwa da su.

Kudurin ya nemi bangarori daban daban da wannan batu ya shafa da su hanzarta tsagaita bude wuta da daukar matakan da suka dace domin kare rayukan yara.

A wannan rana, kwamitin ya yi muhawara kan batun yara da ake mafani da tashin hankali, kana aka zartas da kudurin bai daya, inda aka kalubalanci bangarori daban daban dake musayar wuta da su saki yaran da suka yi garkuwa da su, kana bukaci kasashe membobin kwamitin sulhu da kungiyoyin MDD da na yankuna daban daban na duniya da su yi kokarin tabbatar da ganin yaran da aka yi garkuwa da su sun koma gida sannan ci gaba da rayuwarsu yadda ya kamata.

Ban da haka kuma, kudurin ya ce, kwamitin sulhu na MDD ya damu matuka kan halayyar makarantun da aka yi amfani da su wajen daukar matakan soja, wannan na iya sa a kaiwa irin wadannan makarantu hari, kuma hakan na iya kawo barazana ga tsaron yaran. Kwamitin sulhu na MDD ya kalubalanci kasashe membobinsa da su dauki matakai domin hana irin wadannan dakaru amfani da makarantu don cimma burinsu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China