A 'yan kwanakin baya ne dai bankuna uku na kasar ta Birtaniya, wato Standard Chartered, da Barclays, da kuma HSBC, suka tsunduma cikin zargin amfani da kafofinsu na kudi a tabargazar cin hanci da rashawa da ake zargin jami'an na FIFA da aikatawa.
Hukumomin shari'a na kasar Amurka sun zargi mutane 14 a fannoni 47, ciki hadda jami'an FIFA su 9, wadanda aka zarga da cin hanci da rashawa, da kuma yiwa wasu jami'an sharri, da kuma hallaka kazamin kudi a yayin neman karbar bakuncin kofin kwallon kafa na duniya. Sauran laifuka da ake zarginsu da aikatawa sun hada da gudanar da cinikayya a fannin ayyukan hukumar, da kuma sanya hannu kan kwantiragin ikon watsa wasanni ta talabijin ta hanyoyin da suka sabawa doka.
A daya hannun kuma ana zargin wadannan bankuna uku da taimakawa wadanda ake tuhuma wajen bada hidimar sarrafa kudade tsakanin FIFA da kamfanonin da aka hada kai da su.
Game da wannan zargi, bankunan Standard Chartered, da Barclays sun riga sun soma gudanar da binciken su, ko da yake a nasa bangare bankin HSBC bai yi bayani game da matakin da zai dauka ba tukuna. (Bilkisu)