in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi ya yi umarnin yin bincike game da hari kan gidajen rediyo
2015-05-21 10:33:24 cri

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza, ya yi umarni da a gudanar da bincike, game da harin da aka kaiwa wasu gidajen rediyon kasarsa, yayin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Nkurunziza ya ce, za a zartas da hukunci mai tsanani kan dukkanin wadanda aka samu da hannu cikin barnata gidajen rediyon, da zarar an kammala bincike.

Rahotanni sun ce, an lalata gidan rediyon Rema mai kusanci da gwamnatin kasar, da kuma wasu gidajen rediyo 4, dake da alaka da 'yan adawa. A ranar 14 ga watan nan na Mayu, masu yunkurin juyin mulki a kasar ta Burundi, sun yi kokarin karbe gidan rediyo da talabijin mallakar gwamnatin kasar, kafin daga bisani su dakatar da hakan, lokacin da suka tabbata yunkurinsu bai yi nasara ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China