in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi ya kira zaman majalissun dokokin kasa
2015-05-20 10:07:31 cri

Rahotanni daga Burundi, na cewa, shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya rattaba hannu kan wata dokar gaggawa, wadda ta bukaci majalissun dokokin kasar da su gudanar da zama na musamman a ranekun Laraba da Alhamis.

Hakan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan sauke ministocin kasar uku daga mukamansu, aka kuma maye gurbinsu da sabbi. Ko da yake dai ba a bayyana dalilin kiran zaman majalissun ba, a hannu guda dokar kasar ta tanaji rantsar da sabbin ministoci gaban shugaban kasa, da kuma 'yan majalissar dokoki.

Yanzu haka dai Emmanuel Ntahomvukiye ne ya maye gurbin tsohon ministan tsaron kasar Manjo Janar Pontien Gaciyubwenge. Sai kuma Alain Aime Nyamitwe, wanda ya maye gurbin Laurent Kavakure a matsayin ministan harkokin waje, yayin da kuma Irina Inantore ta zamo sabon ministan harkokin cinikayya, bayan sauke Marie Rose Nizigiyimana.

Sauye-sauyen da shugaba Nkurunziza ya yi wa majalissar ministocin nasa dai sun biyo bayan yunkurin juyin mulkin kasar na 'yan kwanakin baya wanda bai yi nasara ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China