in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan kasashe daban daban sun jinjinawa jawabin da shugaban kasar Sin ya gabatar a taron shugabannin kasashen Asiya da Afrika
2015-04-23 09:42:41 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai lakabin "habaka ra'ayin Bandung, da inganta hadin gwiwa mai kawo moriyar juna" a gun taron shugabannin kasashen Asiya da Afrika da aka kira a birnin Jakarta na kasar Indonesiya.

Ya yin zaman taron na safiyar jiya Laraba, shugaba Xi ya gabatar da wasu shawarwari 3 game da aikin habaka ra'ayin Bandung, kana ya bayyana matakan taimakawa kasashe masu tasowa na Asiya da Afrika a nan gaba.

Da yake tsokaci game da jawabin na shugaba Xi, tsohon sakataren firaminsitan kasar Malaysia Ei Sun Oh, ya ce shugaba Xi ya nanata ra'ayin Bandung game da girmama juna tsakanin kasashen duniya, matakin dake da ma'ana matuka a halin da ake ciki na yunkurin neman mallake duniya.

Shi ma wani masanin harkokin waje daga jami'ar Nairobin kasar Kenya Patrick Maluki, cewa ya yi sabon ra'ayin Bandung zai ba da kwarin gwiwa ga kasashen Asiya da na Afrika, wajen cimma burinsu na tabbatar da wadata a fannin tattalin arziki, da farfado da ayyukan siyasa, da kuma neman samun bunkasuwa mai dorewa.

A nasa bangare masanin harkokin Asiya na jami'ar Monash ta kasar Australia Greg Barton, cewa ya yi a cikin jawabin Xi, ana iya gane cewa, shugabannin kasar Sin za su kara damar taimakawa kasashen duniya, musamman ma kasashen Afrika wajen neman samun bunkasuwa, matakin da a ganin sa zai haifar da makoma mai kyau. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China