in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afirka ta kudu ya ce ba za a kori 'yan kasashen waje ba
2015-04-19 17:41:36 cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, kasar sa ba za ta kori ko wane dan kasar waje ba, matakin da aka dauka na nuna kiyayya ga 'yan kasashen waje wasu mutane kalilan ne masu tsatsauran ra'ayi suka yi kawai.

Yayin da Zuma ya kai ziyara a wani sansanin 'yan gudun hijira a Durban ya ce, abin da ya fi muhimmanci shi ne kwantar da tarzoma da aka tayar, idan ba haka ba, 'yan kasashen waje ba za su kwantar da hankalinsu su tsaya a kasar ba, game da wasu 'yan kasashen waje wadanda suka yanke shawarar komawa kasashensu, yace ana maraba da su dawo idan tarzoma ta kwanta.

Ban da haka, shugaba Zuma ya kuma soke ziyarar da zai yi a Indonesiya, don warware wannan matsala.

Gwamnatin ta nanata cewa, za ta dauki matakai da suka wajaba don tabbatar da lafiyar 'yan kasashen waje, amma wasu kasashen Afrika sun fara janye jama'arsu daga Afrika ta kudu. Jakadan kasar Zimbabwe dake Afrika ta kudu ya ce, Zimbabwe za ta janye jama'arta 1000 wadanda da rikici ya ritsa da su. Malawi ita ma ta fara janye jama'arta. Ban da hakak kuma, kasashen Mazombique, Somaliya, Kenya da Najeriya su ma za su janye jama'arsu.

A kwanan baya, an tada rikicin korar 'yan kasashen waje a wasu wurare a Afrika ta kudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 6, yayin da wasu fiye da 10 suka raunuta, inda kuma aka washe daruruwan shagunan da 'yan kasashen waje ke gudanar, dubu-dubatar 'yan kasashen waje sun rasa gidajensu. An ce, mutanen da suka fi fuskantar rikicin sun fito daga kasashen Mozambique, Malawi, Somaliya, Najeriya, Zimbabwe da Habasha da dai sauran kasashen Afrika. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China