A cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu daga sfishinsa a Abuja, tsohon shugaban mulkin soja yanzu kuma zababben shugaba a karkashin jam'iyyar APC, yace ofishin jakadancin Nigeriya ya dauki matakin da ya dace na shawartan duk 'yan Nigeriya da su rufe shagunansu tare da kaurace ma yawo a garin kowa ya zauna a gida.
Muhammadu Buhari yace 'yan Nigeriya a Afrika ta kudu ya kamata su bi doka da oda na wannan kasa mai masaukinsu. Ya kuma yaba ma gwamnatin Nigeriya game da shawarar da ta yanke na sa ido kwarai akan duk wani cigaba dake wakana a kasar ta Afrika ta kudu tare da kwaso 'yan kasar ta zuwa gida da zaran an ga al'amurra zasu kazanta. (Fatimah Jibril)