Wannan shawarar da Ma Yuhua ta gabatar ta samu martani daga wajen mataimakin shugaban jihar Ningxia Wang Heshan, inda ya bayyana cewa, yanzu gwamnatin jihar tana yin nazari kan batun yin ritaya na likitocin da ke yankunan karkara da kuma yadda za a kula da su bayan ritayar su, a kokarin fitar da manufofin da abin ya shafa tun da wuri. Wang yana mai cewa,
"Gwamnatin mu za ta ci gaba da yin nazari kan wasu batutuwa, kamar nawa ne za a biya likitoci tsoffi, kuma wa zai biya kudin, da dai sauransu. Bayan da muka tabbatar da wadannan batutuwa, to za mu yi kokarin fitar da manufar da abin ya shafa a farkon rabin shekarar bana."
Yayin da Ma Yuhua ta zanta da wakilin mu bayan tattaunawar, ta bayyana cewa, matakin da gwamnatin jihar Ningxia za ta dauka buri ne na dukkan likitocin da ke yankunan karkara, don haka zai ba mu kwarin gwiwa sosai. Matakin kuwa zai ba da taimako wajen kyautata kwarewar aikin likitanci na yankunan karkara. Hakan tana fatan za a iya kammala wannan tsarin kiwo lafiya na kanana wurare a sauran yankunan kasar Sin.
A matsayinsu na wakilan jama'ar kasar Sin, su kan sha aiki kwarai a yayin taron shekara shekara na NPC na tsawon kwanaki goma. A ranar shida ga wata, ban da shirya taron tattaunawa, tawagar wakilan jama'ar jihar Ningxia ita ma ta kira wani taron manema labaru, inda Ma Yuhua ta jawo hankulan dimbin kafofin watsa labaru. Ma Yuhua ta ce,
"A matsayina na wata likita da ke yankin karkara, na yi matukar farin ciki da ba da hidima ga jama'a wajen kiwon lafiyar su. Haka kuma a matsayina na wata wakiliyar jama'ar kasar Sin, abin farin ciki shi ne na iya bayyana ra'ayoyin likitocin da ke yankunan karkara da kuma fatansu a yayin taron NPC. Sabo da haka, ban da ba da jiyya ga mazauna yankunan karkara, ni ma zan yi kokarin gabatar da kyawawan shawarwari a madadin jama'a, ta yadda zan iya biyan bukatunsu gwargwadon iyakacin karfina." (Kande Gao)