150330-Ma-Yuhua-ta-nuna-kulawa-kan-tsarin-kiwon-lafiya-na-kananan-wurare-Kande.m4a
|
"Yanzu ana ta kyautata aikin ba da hidima na kananan wuraren kasar Sin, wanda ya kawo sauki da kuma adalci ga al'umman kasa wajen ganin likita. Sai dai ana fuskantar wassu matsaloli, kamar rashin kyakkyawan tsarin yin ritaya ga likitocin da ke yankunan karkara."
Mai maganan nan ita ce Ma Yuhua mai shekaru 47 da haihuwa daga gundumar Tongxin ta jihar Ningxia da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Ta kuma fadi haka ne a ranar shida ga watan Maris na bana a cikin wata tattaunawar wakilan jihar Ningxia da suka zo birnin Beijing don halartar taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC.
Ranar 6 ga watan Maris rana ce ta biyu bayan kaddamar da taron NPC na bana, inda tawagogin wakilan larduna daban daban suka tattauna kan rahoton gwamnatin aiki da firaminista Li Keqiang ya gabatar a ranar 5 ga wata. A cikin rahoton kuma, an tanadi cewa, za a kara yawan kudin shiga na likitocin da ke yankunan karkara, wanda ya faranta ran Ma Yuhua sosai. Kuma wannan ya sheda cewa, yawan kudin da wani likitan da ke aiki a wani kauyen mai mutane 2000 zai karu da Yuan dubu 10 a ko wace shekara. Ma Yuhua ta furta cewa,
"Abin da ya faranta mini rai shi ne, an mai da hankali kan batunmu likitocin da ke yankunan karkara, har ma an shigar da shi cikin rahoton aikin gwamnatin mu, inda aka tanadi cewa, za a kara yawan kudin shiga na likitocin. Wannan ya sheda muhimmancin da kasar mu ke nunawa likitocin da ke yankunan karkara."
A cikin jawabinta a yayin taron tattaunawa, Ma Yuhua ta sake jaddada bukatar kyautata tsarin ba da hidima ga aikin kiwon lafiyar jama'a na kananan wurare cikin gaggawa, abinda ya hada da ciki batun gaggauta aikin gudanarwa kan kiwon lafiya a yankunan karkara, da kafa tsarin ba da tabbaci ga likitocin da ke yankunan karkara bayan ritayar su. A waje daya kuma, Ma Yuhua ta ba da shawarar shigar da nagartattun likitocin da ke yankunan karkara cikin tsarin cibiyar kiwon lafiya ta gunduma bisa hanyar horar da likitocin da kuma ma su jarrabawa. Ma ta kara da cewa,
"Idan ba a iya warware matsalar tsarin yin ritaya na likitocin da ke yankunan karara ba, to likitoci matasa ba za su iya samun guraban aikin yi ba yi sakamakon rashin ritaya da tsoffin likitocin suka yi. Hakan zai kawo cikas ga kyautatuwar aikin ba da hidima na likitocin da ke yankunan karkara, har ma yasa ba'a iya samun jiyya yadda ya kamata a kauyuka wasu lokuta."