in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma Yuhua ta bayyana ra'ayin likitoci miliyan daya da ke yankunan karkara a matsayinta ta wakiliyar jama'ar Sin
2015-04-03 16:55:22 cri

A'yan shekarun baya baya nan, gwamnatin kasar Sin tana kara kebe kudade ga aikin ba da jiyya na yankunan karkara, wanda ya sa yawan kudin shiga da likitoci suka samu ya samu karuwa. Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta gundumar Tongxin ta bayar, an ce, yawan kudin da wani likitan da ke yankunan karkara ya kan samu a ko wace shekara ya kan kai Yuan dubu 20 zuwa 30, wanda ya ninka sau biyu ko uku bisa na manoman wurin. Don haka, dimbin likitoci tsoffi ba su son yin ritaya, sakamakon damuwar rasa damar samun kudin shiga da kuma kudin kulawa da tsoffi.

Bayan da Ma Yuhua ta yi nazari kan wannan batu, ta fahimci cewa, likitoci tsoffi sun ki yin ritaya, baya ga likitoci matasa sun gaza samun damar samun guraban aikin yi, wannan shi ne babban cikas da ya kawo wa ci gaban aikin jiyya na yankunan karkara. Don haka, batun kafa tsarin yin ritaya don likitoci tsoffi da ke yankunan karkara ya zama wajibi a yi cikin hanzari.

A gabannin taron shekara-shekara na NPC na bana, likitoci kimanin 50 na jihar Ningxia sun je wajen Ma Yuhua domin bayyana ra'ayoyinsu. Ban da wannan kuma, Ma Yuhua ta samu wata wasika da likitoci 231 da ke yankunan karkara na lardin Zhejiang suka rubuta mata, inda suka bukace ta wajen bayyana ra'ayoyinsu a yayin taron NPC a madadin dukkan likitoci miliyan 1.3 da ke dukkan yankunan karkarar kasar Sin. Hakan ya kara nauyin da ke wuyan Ma Yuhua, ta ce,

"Gaskiya dai, aikin ba da jiyya na kananan wuraren kasar Sin ya samu babban sauyi bisa goyon bayan gwamnatin kasarmu. Yanzu muna da sabbin dakunan kiwon lafiya da na'urorin ba da jiyya, bugu da kari an ba mu horo daga dukkan fannoni domin kyautata kwarewarmu wajen aiki. Amma ina alla alla da za a iya warware matsalar da mu likitocin da ke yankunan karkara ke fuskanta wajen neman samun kulawa bayan ritaya, hakan ba za a bata ran likitoci fiye da miliyan 1.3 da ke yankunan karkara na duk fadin kasarmu."  (Kande Gao)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China