150323-Ma-Yuhua-ta-bayyana-raayin-likitoci-miliyan-daya-dake-yankunan-karkara-a-matsayinta-ta-wakiliyar-jamaar-Sin-Kande.m4a
|
"Mu likitocin da ke yankunan karkara muna zama a madadin uwayen yara da suka rasa mahaifansu mata, da muke kula da su. Yanzu muna tsufa, amma ba a nuna mana wata hanyar da za mu bi bayan da muka yi ritaya ba. Mun dade muna aikin likitanci har na tsawon shekaru gomai, amma har yanzu ba mu san yadda za mu yi a nan gaba ba."
Mai maganan nan shi ne Ma Quanren wani Dattijo mai shekaru 64 da haihuwa, wanda yake aikin likitanci har na tsawon shekaru fiye da 40 a kauyen Lianhe na gundumar Tongxin da ke jihar Ningxia ta kasar Sin. Yanzu shekarunsa kuma sun wuce shekarun yin ritaya bisa doka. A ko da yaushe da ya gamu da Madam Ma Yuhua, wadda ita ma wata likita ce da ke yankunan karkara, kuma wata wakiliyar jama'ar kasar Sin, ya kan tambaye ta kan yaushe ne za a iya fitar da manufar da ta shafi batun yin ritaya da kulawa da tsoffi likitocin da ke yankunan karkara.
Bayan da Ma Yuhua ta zama wakiliyar jama'ar kasar Sin a shekarar 2013, ta kan yi musayar ra'ayoyi kan batun ci gaban aikin jiyya na yankunan karkara tare da Ma Quanren da sauran likitoci fiye da 30 a yayin taron wata wata da a kan yi a garinsu. Ban da wannan kuma, a gabannin taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na ko wace shekara, ta kan tattara likitocin da ke yankunan karkara domin sauraron shawarwarinsu.
A shekarar bana, batun da suka mai da hankali a kai shi ne yadda za a samar da guraban aikin yi ga likitoci matasa kusan 100 da suka kammala karatu a shekarar 2014, wadanda ke da aniyar yin aiki a yankunan karkara, gami da batun yadda za a warware matsalar kulawa da likitoci tsoffi kusan 100, wadanda suka wuce shekarun yin ritaya bisa doka. Wang Jinyong, shugaban cibiyar kula da aikin kiwon lafiya na garin Wang Tuan ya bayyana cewa,
"Ya zuwa yanzu ba a kafa wani tsarin yin ritaya don likitocin da ke yankunan karkara ba, akwai dimbin likitoci da ke ci gaba da aiki, duk da shekarunsu da haihuwa suka wuce 60. Idan za a iya fitar da wannan tsari, to likitoci matasa za su iya samun damar aiki, hakan zai kyautata aikin ba da jiyya, baya ga hakan likitoci tsoffi za su samu kwanciyar hankali."
Yanzu babban abinda ke kawo cikas a batun kyautatuwar aikin jiyya na yankunan karkara shi ne yawan tsaffin likitoci. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, yanzu ana iya samun rabin likitocin da ke yankunan karkara da shekarunsu suka wuce 50, a ciki akwai kashi 40 cikin dari da shekarunsu suka wuce 60, har ma akwai wasu da shekarunsu suka zarce 70 da haihuwa. Domin warware wannan matsala, gwamnatin jihar Ningxia ta dauki matasa 97 a shekarar 2011 domin su koyi ilmin likitanci a jami'a har na tsawon shekaru uku, sannan nan za su gudanar da aikin ba da jiyya a yankunan karkara bayan da suka gama karatu. A shekarar 2014, wadannan dalibai sun gama karatunsu daga jami'a, amma akasarin su ba su samun guraban aikin yi ba.
Ma Yuhua ta yi nazari sosai kan wannan batu, kuma ta bullo da wata shawara a gabannin zuwan ta birnin Beijing don halartar taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar Sin na bana. Domin ganin cewar wannan shawara ta dace da halin da ake ciki, ta tattauna tare da mataimakin shugaban hukumar kiwon lafiya ta gundumar TongXin Shi Jingcai. A ganin Mr. Shi, shawarar da Ma Yuhua ta bullo kan tsarin yin ritaya na likitocin da ke yankunan karkara na da ma'ana sosai. Ya kara da cewa,
"Idan likitocin da ke yankunan karkara suna iya bayar da amfaninsu yadda ya kamata, to za a iya warkar da marasa lafiya na yau da kullum a kananan yankuna, hakan zai sa a iya yin tsimin albarkatu, kuma ba za a iya samun dimbin mutane fiye da kima a manyan asibitoci ba, har ma za mu iya rage yawan kudin da mu kan kebe don ba da tabbaci ga aikin jiyya."