in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma Yuhua na kulawa da yadda ake gudanar da ayyukan jinya a kananan sassa
2015-03-17 16:43:02 cri

Ma Yuhua it ace likita daga dilo a kauyen Luojiahewan, wanda ke da yawan mutane 2400, it ace kuma daya daga cikin likitoci dubu 1300 dake aiki a kauyuka a nan kasar Sin. Ayyukan dake kan Ma Yuhua sun yi yawa sosai, ban da ayyukan yi wa yara allurer rigakafi, da kula da kiwon lafiyar mata, da ba da ilmi kan kiwon lafiya, da yin rigakafin cututtuka masu yaduwa, da bayanin da aka adana na kiwon lafiya da dai sauransu, kuma aikin ba da jinya kan cututtuka marasa tsanani shi ne wani sashe ne na ayyukan nata na yau da kullum.

A wannan rana da yamma, mazauna yauyen biyu sun iso nan dakin ba da jinya.

"Me kike so?"

"Ko akwai maganin kuna?"

"Maganin kuna? Babu, ki yi hakuri."

"Ko akwai maganin Gan Mao Tong?"

"Babu irin maganin."

"Gan Kang fa?"

"Babu, akwai Lian Hua Qing Wen"

"Akwai mana a gida."

A wannan dakin ba da jinya, akwai maganganu irin sama da 300 da asibitin garinsu ya samar. Ma Yuhua ta riga ta tuna da sunayen dukkan maganganun, da kuma amfaninsu da yawansu. Bayan mazaunen kauyen biyu sun tashi, Ma Yuhua ta gayawa wakilinmu cewa,

"Lallai babu wadancan maganganun da suke bukata. Kamar yadda na gaya maka, maganganun da aka samar ba su iya biyan bukatun mazaunen kauyen ba."

Kafin shekaru 28 da suka gabata, Saboda aure Ma Yuhua ta iso nan kauyen Luojiahewan daga gundumar dake makwabtaka. A lokaci, babu likita ne a wannan kauye saboda kudin shiga kadan, da rashin kwararru da suka dace a fannin. A shekarar 1996, a matsayinta na daliba daya tilo da ta kamala karatu a babbar makarantar sakandare, bayan samu horo a makarantar kiwon lafiya sai Ma Yuhua ta soma aikin likita a kauyen.

Daga tafi gidajen mazauna kauyen tare da daukar akwatin maganganu a farko, zuwa kafa bayanin da aka adana game da kiwon lafiya a intanet ga mazauna kauyen a yanzu, a ko da yaushe Ma Yuhua tana mai kula da kiwon lafiyar mazauna kauyen ce da aka yi mata imani kwarai. Yanzu, Ma Yuhua na iya ba da jinya ga mazauna kauyen a dakin jinya nata kamar yadda likitoci na asibitocin birane da garurruka suke, har ma ta iya gudanar da ayyukan sake shigar da kudin ganin likita na mazaunan. Yanzu, sakamakon sauki da ake samar wajen ganin likita da sayen maganganu, mazaunen kauyen dake zo dakin jinya suna ta yi yawa. Ma Jinfang, 'yar shekaru 40 a duniya, ta dade tana samun jinya a nan dakin jinya. Ta gaya wa wakilinmu cewa,

"A yayin da nake kamu da mura, ina jin ciwon kafa, har ma ban iya tsayawa ba. Wannan ciwon na samu ne na tsawon shekaru kusan 7, ciwo ne da ya dade a jiki. Na kasha kudi da yawa ne sakamakon ciwon, a da babu wanda ke ba mu kudin da muka kashe, amma yanzu ba haka ba, bisa sabon tsarin ba da magani na hadin gwiwa idan na kashe kudin RMB 3000, to zan iya samu kudin RMB 2000."

Wannan sabon tsari a bakin Ma Jinfang, wani tsarin ba da magani na hadin gwiwa ne da aka soma gudanar a shekarar 2010, wanda ya shafi dukkan kauyukan kasar Sin. Bisa tsarin, yawan kudin da manoma za su sake shigar wajen kudin da suka kashe don ganin likita zai kai kasha 70 cikin dari.

A shekarar 2013, an zabi Ma Yuhua da ta zama wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. Tun daga lokacin, ta soma gudanar da bincike sosai kan batun karfafa kwarewar tsarin kiwon lafiya na kauyuka. Tana mai ganin cewa,

"Mu likita ne a kauyuka, ko da yake muna gudanar da ayyuka sosai, amma ba a ba mu wani mukamin da ya dace ba, kuma ba mu samu tabbaci wajen zaman rayuwa ba. Ban da wannan kuma, yanayin dakunan jinya na kauyuka ba ya da kyau. A matsayi nan a wata wakiliyar majalisar wakilan jama'a, ina fatan dawo da ra'ayinsu da bukatunsu zuwa nan, da nufin samun kulawa daga wajen shugabannin kasarmu."


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China