150316-Ma-Yuhua-wakiliyar-majalisar-wakilan-jamaar-kasar-Sin-dake-kulawa-da-yadda-ake-gudanar-da-ayyukan-jinya-a-kananan-sassa-Bilki.m4a
|
"A wancan lokacin da muke azumi, da kyar ake iya neman mota ne. Wancan yaro idanunsa rufe suke, kuma jijiyoyin jini ke bugewa kadan kadan."
A safiyar wata rana da karfe 3 a watan Azumi na shekarar 2013, wani miji da mata sun rushe cikin dakin ba da jinya na kauyen Luojiahewan na jihar Ningxia, tare da daukar 'dansu, wanda shekarun haihuwarsa suka kai 3. Wannan karamin yaro yay i suma sakamakon zazzabi mai zafi, har ma jikinsa ya yi kyarma. Ma Yuhua, wadda mai aikin likita ce ta waiwayi cewa,
"Babu gudan kankara a lokacin, sai babu dabara ne na zabi hanyar amfani da barasa. Na gaya wa mama da ta cuda hannayen 'danta, a sa'i daya kuma na shafar barasa a kan jikinsa. Muna ta yi haka, muna ta yi haka, bayan mintoci 20, wannan yaro ya bude idannunsa, ko da yake ban iya tsayawa ba saboda na yi labe cikin dogon lokaci, amma na yi farin ciki sosai."
A ganin Ma Yuhua, ayyukan da take yi na tsawon shekaru 20 sun sanya ta kara fahimtar muhimmanci wajen kafa dakunan ba da jinya a kauyuka, ban da wannan kuma ta sani cewa, na'urorin kiwon lafiya na kauyuka ba su da inganci ne, kuma ba a kai ga wani matsayi yadda ya kamata ba a kan aikin ba da jinya a kauyuka.
Kauyen Luojiahewan da Ma Yuhua ke zama yana karkashin jagorancin gundumar Tongxin ta jihar Ningxia dake arewa maso yammacin kasar Sin, gundumar din ta kasance daga daga cikin gundumomin da suka fi fama da talauci a nan kasar Sin. Sakamakon yanayin halittu da take ciki, hukumar shirin samar da abinci ta duniya wato WFP ta taba mai da gundumar a matsayin wurin da ba sa dacewar rayuwar dan Adam.