in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyara a sasanin sojojin kasar Sin masu kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2015-03-03 17:36:42 cri

Ranar 28 ga watan Fabrairu na bana ta kasance rana ta biyu bayan da rukunin farko na bataliyar sojojin kasar Sin ya isa wurin aikinsu dake Juba. A waccan rana an yi ruwa kamar da bakin kwarya, wanda ya kasance tamkar wani bikin marhabin ne ga wadannan sojojin. Duk da cewa a waccan ranar iska mai karfi ta kifar da tankuna da yawa, amma a ganin sojan kasar Sin mai suna Yang Zean, wannan ba wani abu ba ne.

"Yayin da muke samun horo a kasar Sin, mun sha wahala sosai, domin yanayi yana da zafi, kana horon ya sa mun gaji sosai. Tun da muka jure wadannan wahalhalu a gida, to, matsalar da muke fuskanta a ketare ba wani abu ba ne. Duk da cewa za mu jure wahala a nan, amma jama'ar kasarmu sun ba mu yabo sosai, wanda ya karfafa gwiwarmu, don mu gudanar da aikinmu yadda ya kamata."

Yu Bin, wani likita ne mai kula da aikin shawo kan bazuwar annoba. Yanzu yana kokarin fesa ruwan magani ga tankunan sasanin. A cewarsa, ana gudanar da wannan aikin a kai a kai.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China