150303-ziyara-a-sasanin-sojojin-kasar-sin-masu-kiyaye-zaman-lafiya-a-sudan-ta-kudu-bello.m4a
|
Tun bayan da ta samu 'yancin kai a watan Yulin shekarar 2011, kasar Sudan ta Kudu ta dade tana fama da tashin hankali, lamarin da ya haddasa rasa rayuka da dama, da tilasta jama'a fiye da miliyan 1 yin gudun hijira. Ganin yanayin da kasar take ciki ya sa kwamitin sulhu na MDD ya yanke shawarar tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar a watan Mayu na shekarar bara wanda a ciki aka gayyaci kasar Sin don ta tura bataliya guda zuwa Sudan ta Kudu.