in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COMESA na kokarin tsai da kudin amfani bai daya nan da karshen 2018
2015-02-25 10:17:38 cri

Cibiyar ciniki mafi girma a Afrika na gabashi da kudancin nahiyar wato COMESA a ranar Talatar nan ta sanar da cewa, ta tsai da kudurin samar da kudin amfani bai daya ga kasashe mambobinta 19 nan da karshen shekara ta 2018.

Shugaban makarantar cibiyar Ibrahim Zeidi ya sheida wa Xinhua a Nairobi cewa, kasashe mambobi a yanzu haka suna aiwatar da dukkan shiri ta bangatren tattalin arziki domin cimma wannan nufi na kudi bai daya.

Shi dai kudi bai daya zai rage tsadar hada hadar tsakanin kasashe mambobi, in ji Mr. Zeidi a taron nazari karo na 4 da cibiyar ta shirya.

Taron na yini uku ya samu halartar wakilai 200 daga cibiyoyin hada hadar ciniki domin yin nazarin hanyoyin hanzarta shirin yankunan da aiwatar da su ta hanyar amfani kayayyakin lura da tantancewa. Ibrahim Zeidi ya ce, kasashe mambobi za su daidaita tsarin kudadensu domin nasarar wannan shiri. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China