Kungiyar OECD ta gabatar da rahoton ne mai taken "Manufar samun bunkasuwa" wanda ya yi nazari game da aikin yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arzikin kasa da kasa. Rahoton ya ce, gibin dake tsakanin matsakaicin yawan kudin da ake samu daga ma'aunin GDP na kasar Sin, da na manyan kasashe mambobin kungiyar OECD na raguwa, tun daga shekarar 2008 zuwa 2013.
Kaza lika rahoton ya ce Sin ta samu babban ci gaba a aikin kwaskwarima a manyan fannoni. Ciki hadda bangaren bude kofa ga jarin sassa masu zaman kansu a fannoni da dama, an kuma saukaka aikin bincike kan jari daga kasashen waje. Bugu da kari an raya sha'anin bada ilmi mai inganci, da kuma kwaskwarima kan farashin kudin ruwa, don kara samar da moriya ga masu ajiyar kudi a bankuna. (Zainab)