in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutanen Somaliya sama da dubu 700 na fuskantar tsananin karancin abinci
2015-01-30 12:31:48 cri

Wata kididdigar MDD na nuni da cewar, a kalla mutane dubu 731 ne ke fuskantar matsalar karancin abinci a wurare dabam-dabam a kasar Somaliya, duk da yake cewar wadansu yankunan, an samu saukin matsalar.

Wani binciken hadin gwiwa na baya-bayan nan wanda ke da sa hannu na hukumar binciken wadatar abinci mai gina jiki ta Somalia a karkashin sa ido na hukumar samar da abinci da ayyukan gona ta MDD da kuma hukumar gargadin kamfar abinci yana nuni da cewar, adadin jama'ar dake fuskantar karancin abinci yana nuni da cewar, an samu raguwar matsalar da kashi 29 bisa dari daga hasashen da aka yi na watan Yuli zuwa Disambar shekarar bara.

Rahoton wanda ya samu madogarar MDD ya yi gargadi cewar, idan har ba'a samu taimakon agaji ba, wasu mutane fiye da miliyan 2.3 za su fada cikin barazanar karancin abinci

Rahoton ya ce, duk da yake cewar, an samu wadatar abinci da albarkar kiwon dabbobi da kuma daidaituwar farashin abinci, mutane da yawa a Somaliyar za su fada cikin matsalar karancin abinci nan da zuwa watan Yuni.

Rahoton ya ce, akwai kananan yara kimanin dubu 38, wadanda ba su samun abinci mai gina jiki, duk kuwa da yake cewar, an samu raguwar wadanda ke fama da matsalar karancin abincin mai gina jiki a cikin tsawon watanni 6.

Hakazalika rahoton ya bankado cewar, yara kusan dubu 203 suka shiga cikin hali na bukatar taimako na gaggawa, kuma matsalar ta fi yin kamari a bangaren jama'a da suka rasa muhallansu, inda suka hada da garuruwan Bossaso, Baidoa da Doolow, to amma kuma a wasu wurare kamar su Mogadishu, Kismayo, da Dhbley, an samu wadatar abinci mai gina jiki

Mai gudanar da ayyukan agaji na MDD a kasar Somaliya Phillipe Lazzarini ya ce, taimako da kasar ta samu daga kasashen duniya ya taimaka wajen bayar da agaji a daidai lokacin da ake bukatar agajin, kuma hakan ya hana a fada cikin masifar karancin abinci

Ya ce, a shekarar 2015 da muke ciki, hukumar agajin ta nemi taimakon agaji na zunzurtun kudi har miliyan 863 na dalar Amurka domin a ceci rayuwa, tare da kare lafiyar jama'ar da suka rasa muhallansu, da kuma samar da kafofi na magance matsalolin masu dorewa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China