Kananan yara da dama ne suka shiga gasar tseren cikin tabo ta shekarar 2015 da ya gudana a ranar 18 ga watan Janairun wannan shekara a wajen arewacin birnin Hararen kasar Zimbabwe.
Shekaru uku ke nan ana gudanar da gasar da aka saba yinta a ko wace shekara a kasar ta Zimbabawe. Daruruwan mutane daga rukunin shekaru daban-daban galibi masu hannu da shuni ne suka shiga gasar ta bana, wadda ke cike da ban sha'awa na nuna kauna ga wasannin motsa jiki da yanayin muhallin da ke kewaye da dan-adam.(Ibrahim Yaya)