in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta shirya bikin bada lambar yabo ga fitattun likitocin da ke ba da taimako a kasashen waje
2015-01-07 17:26:20 cri


Jiya ranar 6 ga wata, an shirya wani bikin bada lambar yabo ga fitattun likitocin dake bada taimako a kasashen waje a nan birnin Beijing. A cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata, kungiyoyin ba da jinya da kasar Sin ta tura a kasashen ketare sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a kasashe da yankuna fiye da 60, tare da warkar da mutane fiye da miliyan 200 bisa kwarewarsu kan aiki da kuma kaunar da suka nuna wa jama'ar wadannan wurare. Sabo da haka, Dr. Bernhard Schwartlander, wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da ke kasar Sin ya yaba wa kasar Sin game da babbar gudummawar da ta bayar a fannin kiwon lafiyar jama'ar kasashen duniya.

likitocin ba da jinya da kasar Sin ta tura a kasashen waje, wata muhimmiyar hanya ce ta hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, wadda kuma ta riga ta gudanar da ayyukan jiyya har na tsawon shekaru 51. Tun bayan da kasar Sin ta fara aikewa da kungiyarta ta farko a fannin aikin jinya zuwa kasar Aljeriya a shekara ta 1963, daya bayan daya gwamnatin kasar Sin ta tura likitocinta fiye da dubu 20 zuwa kasashe da yankuna 67. Kuma kawo karshen shekarar 2013, yawan mutanen dake kasashe masu tasowa da kungiyoyin jiyya na kasar Sin suka warkar ya zarce miliyan 260, baya ga horar da dubu dubban likitoci da ma'aikatan jiyya na wadannan kasashe. A halin yanzu dai ma, akwai ma'aikatan jiyya na kasar Sin kimamin 1100 da ke gudanar da ayyukansu a kasashe fiye da 50.

Hakan ya sa Dr. Bernhard Schwartlander, wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da ke kasar Sin ya yi wa kasar Sin jinjina ta musammun a kan nasarorin da ta samu a fannin samar da taimakon jinya ga kasashen ketare. Yana mai cewa,

"Hakika, abokaina da ke kasashen Afirka sun gaya min cewa, yayin da aka haife su, likitocin kasar Sin ne suka taimaka wa iyayensu a lokacin. Ban da haka, a tsawon wadannan shekaru masu yawa, likitocin kasar Sin ne suka yi musu jinya, har ma yanzu suna kulawa da iyayensu tsoffi a cikin asibitocin da aka gina bisa taimakon kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun sheda dankon zumunci a tsakaninsu da kasashen Afirka bisa kokarin da suka yi cikin tsawon shekaru 50 da suka gabata, don haka kungiyar WHO ta nuna babban yabo ga kasar Sin da muhimmiyar gudummawa da take bayarwa ga lafiyar jama'ar duk duniya."

Bisa labarin da aka bayar, an ce, ko da yake kungiyoyin aikin jiyya da kasar Sin ta tura sun shafi dukkan manyan nahiyoyin duniya biyar, amma yawancinsu an tura su ne zuwa kasashen Afirkan da ke fama da matsalar karancin likitoci da magani. A cikin shekaru 51 da suka gabata, an samu likitoci Sinawa 50 da suka rasa rayukansu a ketare. Wang Liji, mataimakin shugaban ofishin kula da hadin gwiwa da kasa da kasa na kwamitin kula da kiwon lafiya da haihuwa na kasar Sin ya bayyana cewa, ban da yanayin aiki da zaman rayuwa mai tsanani, ma'aikatan jiyya su kan fuskanci hadarin kamuwa da ciwon malariya, kwalara da kuma sida. Wang Liji ya kara da cewa,

"Ana fama da cutar malariya mai tsanani a tsakiyar Afirka, don haka yawancin 'yan kungiyar jinya na kasar Sin sun taba kamuwa da cutar, wadda ta rika sanya jikinsu rawa da kuma zafin jiki kullum. Bugu da kari, wasu kasashen Afirka suna fama da ciwon sida mai tsanani, yayin da likitoci suke yi wa masu fama da wannan cutar tiyata, su kan fuskanci hadura masu tsanani, idan allura ta soke su, ko kuma jinin mutanen ya tsirta musu a ido. Haka zalika, wasu kasashen da ke tsakiyar Afirka na fama da yake-yake a shekarun nan, likitocinmu su kan ji amon bindigogi da boma-bomai, har ma wasu sun mutu sakamakon wadannan tashe tashen hankali"

A watan Fabrairun shekarar bara, cutar Ebola mai saurin kisa ta barke a kasashen da ke yammmacin Afirka. Domin taimaka musu wajen yaki da cutar, kasar Sin ta samar da taimakon agaji har sau hudu da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan miliyan 750, baya ga aikewa da rukunonin kwararrun likitoci kusan goma, da kuma masu aikin jinya fiye da 1000. Dr. Schwartlander yana ganin cewa, kasar Sin ta ba da muhimmin tasiri wajen taimakawa yammacin Afirka don shawo kan cutar Ebola. Ya ce,

"Bayan farko farkon barkewar cutar Ebola, kasar Sin ta fara samar wa yammacin Afirka dimbin albarkatun jinya da kiwon lafiyar jama'a, don haka kungiyar WHO ta nuna matukar godiya gare ta. Ban da samar da taimakon kudi da kayayyaki, kasar Sin ta tallafa wa kasashen da ke yammacin Afirka wajen raya muhimman ayyukan more rayuwa da dakunan gwaje-gwaje. Abin mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta tura nagartattun likitoci da masu aikin jiyya nata zuwa kasashe masu fama da cutar, domin kara karfin wadannan kasashe ta fuskar kiwon lafiya, a kokarin samun nasarar yaki da cutar tare."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China