A wannan yayin bikin Kyakkyawar Afirka, an shirya kananan bukukuwa iri daban daban kamar su: bikin nune-nunen kide-kide da raye-rayen Afirka, kafa kasuwar sayar da kayayyakin da suke da nasaba da kasashen Afirka, tara kudin kyauta ga wata makarantar da ake ginawa a kasar Kenya da sauran yaran kasashen Afirka, dandanlin tattaunawa, inda dalibai suka yi amfani da harshen Turanci wajen tattauna batutuwan bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka, kiyaye muhalli da batun cutar Ebola da dai makamatansu, har ma an bude wasu dakunan nune-nunen al'adun kasashen Najeriya, Kenya, Masar, Afirka ta kudu da Tanzaniya domin kara wa yara ilmin kasashen Afirka.
Dadin dadawa, an shirya wasu wasannin yara, ta yadda dalibai za su iya samun fahimta kan kasashen Afirka a lokacin da suke wasa. (Sanusi Chen, Ibrahim Yaya)