A wajen wannan biki, wani malami mai suna Fang Qi wanda ya zo daga kasar Sin, ya nunawa 'yan Najeriya yadda ake yin zane-zanen gargajiya na kasar Sin ta hanyar da ta dace, sa'an nan 'yan Najeriya da dama suka gwada da kansu domin kara fahimtar al'adun gargajiyar kasar Sin. Daga bisani, malami Fang Qi ya nuna fasahar dafa shayi wato Tea a turance a gaban masu kallo 'yan Najeriya, inda suka samu damar dandana shayi na kasar Sin .
Mohammed Suleiman, wani babban jami'i daga hukumar yada al'adun gargajiya dake birnin Abuja ya bayyana ra'ayinsa game da wannan biki.