in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nuna fasahohin zane-zanen gargajiya da dafa abun shayi na kasar Sin a birnin Abuja na tarayyar Najeriya
2014-07-01 17:11:01 cri

A ranar Litinin 30 ga wata da yamma, a cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, aka yi wani biki na nuna fasahohin zane-zanen gargajiya da samar da shayi na kasar Sin, bikin da ya samu halartar masu sha'awar al'adun Sin daga bangarori daban-daban na Najeriya. Wakilinmu Murtala na dauke da karin bayani.

A wajen wannan biki, wani malami mai suna Fang Qi wanda ya zo daga kasar Sin, ya nunawa 'yan Najeriya yadda ake yin zane-zanen gargajiya na kasar Sin ta hanyar da ta dace, sa'an nan 'yan Najeriya da dama suka gwada da kansu domin kara fahimtar al'adun gargajiyar kasar Sin. Daga bisani, malami Fang Qi ya nuna fasahar dafa shayi wato Tea a turance a gaban masu kallo 'yan Najeriya, inda suka samu damar dandana shayi na kasar Sin .

Mohammed Suleiman, wani babban jami'i daga hukumar yada al'adun gargajiya dake birnin Abuja ya bayyana ra'ayinsa game da wannan biki.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China