in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun harbe 'yan Boko Haram 9
2014-06-03 09:34:26 cri

Rundunar sojin Najeriya ta ce, dakarunta sun samu nasarar harbe 'yan kungiyar Boko Haram su 9, yayin wani dauki ba dadi a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar manjo janar Chris Olukolade wanda ya shaidawa manema labaru hakan ya kara da cewa, sojojin sun hallaka mayakan kungiyar ne yayin da suke kokarin kaiwa kauyukan Buratai da Kawuri dake jihar ta Borno hari.

Olukolade ya ce, a dauki ba dadin da bangarorin biyu suka yi a kauyen Buratai dake karamar hukumar Biu, sojojin sun harbe 'yan Boko Haram 4, suka kuma kame daya da ransa. A Kawuri kuwa, sojojin sun harbe mayakan ne su 5. Baya ga bindigogi kirar AK 47 da motoci 2 da sojojin suka kwace.

A wani ci gaban kuma Olukolade ya ce, an samu nasarar cafke wanda ake zargi, da kitsa harin bam a ranar Lahadi, wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane 18, a wani gidan kallon wasan kwallon kafa dake Kabang a karamar hukumar Mubin jihar Adamawa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China