Handan birnin ne da ke kudancin lardin Heibei a arewacin kasar Sin, wanda ke da fadin kilomita dubu 12 da kuma al'umma miliyan 9.63. Handan birni ne da ya shahara da dadadden tarihinsa, inda tun shekaru sama da 8000 da suka wuce ne, 'yan Adam sun fara zama a yankin har ma sun fara samun wayin kansu, kuma a shekaru fiye da 3100 da suka wuce ne, aka kafa birnin.
1 2