in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UEMOA da CPLP sun gamsu da yadda zabe ya gudana a Guinea-Bissau
2014-04-16 10:16:40 cri

Kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) da kuma gamayyar kasashen dake amfani da harshen Portugal (CPLP) sun nuna jin dadinsu kan yadda aka gudanar da zabubukan shugaban kasa da na 'yan majalisa a ranar Lahadi a kasar Guinea-Bissau.

Wadannan zabubuka sun gudana cikin 'yanci da gaskiya kuma cikin adalci, in ji shugabn tawagar sanya ido ta kungiyar UEMOA, mista Lancina Dosso tare da yin kira ga jam'iyyun siyasa da 'yan takara da su girmama sakamakon zabe.

A nata bangare, tawagar sanya ido kan zabe ta CPLP ta yi imani da kishin kasa da adalci da aka nuna a yayin wadannan zabubuka.

A lokacin yakin neman zabe, har ma a lokacin zabe, ba'a samu hadari ko guda ba, in ji mista Leonardo Simao, shugaban tawagar sanya ido kan zabe ta CPLP. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China