Shugaban Bankin duniya Kim Yong ya bayyana a ran 9 ga wata cewa, Bankin duniya yana sanya ran kara hadin kai da kasar Sin, da koyon juna da aiwatar da kyakkyawan sakamakon da suka samu zuwa sauran kasashe.
Kim Yong ya yi wannan bayani ne a gun wani taron manema labaru a jajibirin taron shekara-shekara na lokacin bazara na Bankin Duniya da Asusun ba da lamuni na IMF. A cewarsa, ko da yake a halin yanzu kasar Sin ba ta bukatar samun kudi daga Bankin duniya, amma Sin tana iya samun rancen kudi daga Bankin duniya, bisa dalilin gudanar da hadin kai yadda ya kamata a tsakanin bangarorin biyu a fannoni da dama a yau da kullum.
Kim Yong ya ci gaba da cewa, ko da yake saurin karuwar tattalin arzikin Sin ya ragu kadan, amma matsayin da gwamnatin Sin take rike da shi wajen yin gyare-gyare kan tsari ya burge jama'a. (Danladi)