in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kara wa juna sani tsakanin Sin da Holland game da hadin gwiwarsu da Afirka
2014-03-31 15:01:42 cri
A yau Litinin ne aka gudanar da wani taron kara wa juna sani tsakanin kwalejin nazarin dangantakar kasa da kasa ta jami'ar Peking, da cibiyar nazarin harkokin Afirka ta jami'ar Peking ta kasar Sin, da kuma cibiyar nazarin harkokin Afirka ta jami'ar Leiden ta kasar Holland, dangane da ra'ayoyinsu kan harkokin kasashen Afirka, da kuma hadin gwiwarsu tare da kasashen nahiyar.

A yayin taron, He Wenping, masaniyar kasar Sin wadda ke nazarin harkokin nahiyar Afirka ta bayyana cewa, tun lokacin da aka shiga karni na 21, taimakon da kasar Sin ke baiwa kasashen Afirka, da kuma hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu, ke ci gaba da karuwa, kuma kasar Sin ta fi mai da hankali kan bukatun kasashen Afirka don samun bunkasuwa ta hanyar samar da taimako gare su.

A nasa bangare, Mr. Meine Piter van Dijk, masanin kasar Holland ya bayyana cewa, kasashen Turai sun fi mai da hankali kan taimaka wa kasashen Afirka, a fagen bunkasa tattalin arzikinsu, ta yadda kasashen za su samu damar gudanar da harkokinsu na gida yadda ya kamata. A kuma halin da ake ciki, kasashen Turai na kyautata manufofinsu na taimakawa kasashen Afirka don gane da saurin bunkasuwarsu.

Bayan taron, tsohon wakilin musamman na kasar Sin mai kula da harkokin nahiyar Afirka Liu Guijin ya gaya wa wakiliyarmu cewa, ko da yake cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, kasashen Afrika na ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri, a hannu guda akwai kalubaloli da dama dake fuskantar nahiyar, ciki hadda batun kokarin yaki da talauci da dai sauransu. Don haka ne ma a cewarsa, ya kamata kasashen Afirka su gudanar da gyare-gyare, da daukar matakan samun bunkasuwa yadda ya kamata, don tabbatar da dauwamammen ci gabansu a nan gaba.

Taron wanda ya gudana a nan Beijing ya samu halartar shahararrun masanan daga kasashen Sin, da Holland da kuma Afirka, wadanda kuma suka bayyana ra'ayoyi, da kuma hasashensu game da batutuwan da aka tattauna. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China