Lu Shaye ya bayyana a gun taron tattaunawa kan harkokin diplomasiyya da aka yi a kan shafin internet a wannan rana cewa, yana fatan bangarori daban daban za su kara sa lura kan nahiyar Afirka, da kuma inganta dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka zuwa wani sabon matsayi.
Lu Shaye ya nuna cewa, a sabon karnin da ake ciki, an samu babban ci gaba kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka, yawan kudin ciniki a tsakaninsu da aka samu a kowace shekara ya kai kimanin dala biliyan 200, kana yawan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka ya kai dala biliyan 17. Ban da wannan kuma, an kara yin mu'amala a tsakanin jama'ar bangarorin biyu. Yawan Sinawa da suke zuwa kasar Afirka ta kudu a kowace shekara ya kai dubu 100, kana yawansu da suka je kasar Seychelles ya kai dubu 4, adadin da ya ninka cikin sauri. (Zainab)