in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kaddamar da wani gagarumin kamfel din kai harin soja don kawo karshen ayyukan 'yan tawaye
2013-11-13 10:16:31 cri

Ministan tsaron kasar Sudan Abdul-Rahim Mohamed Hussein ya ayyana fara wani gagarumin kamfel din kai harin soja, da nufin kawo karshen ayyukan masu tayar da kayar baya a yankin Darfur da jihohin Blue Nile da kudancin Kordofan da ke iyaka da kasar Sudan ta Kudu.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata cikin wata sanarwa da ya gabatarwa majalisar dokokin kasar, inda ya ce, kasarsa ta kimtsa kuma ta tura dakaru zuwa sassa daban-daban na wadannan yankunan da nufin dakile ayyukan masu tayar da kayar baya.

Bugu da kari, ya zargi 'yan tawayen Revolutionaey Front, wadanda ke kwance da kungiyoyi hudu masu dauke da makamai da zummar halaka jama'a da sace mutane a wasu manyan birane.

Tun da farko dai shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan, ya lashi takwabin kawo karshen dukkan tashin hankali da fadace-fadacen da ake samu tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a dukkan sassan kasar ya zuwa karshen shekarar 2014. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China