Sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro da jamhuriyar Afrika ta tsakiya ke fuskanta, kasar Cote D'Ivoire ta yanke shawarar tura jirgin saman musamman domin kwashe jama'arta daga jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
Ana ta yi tashin hankali a jamhuriyar Afrika ta tsakiya. A watan Maris na bana ne, 'yan tawayen Seleka suka hambarar da mulkin shugaban kasar François Bozizé. A cikin Afrilu, an kafa gwamnatin wucin gadi ta kasar, inda aka zabi Michel Djotodia jagoran 'yan Seleka a matsayin shugaban kasa na wucin gadi na kasar. Kwanan baya, an kara tsananta rikicin dake tsakanin dakarun 'yan Seleka da dakaru masu tsaron kansu na kasar, lamarin da ya haddasa hargitsin jin kai mai tsanani.
A ranar 26 ga wata, babban magatakardan M.D.D. Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa, inda ya nuna mamaki sosai kan rikicin da aka ta samu a Afrika ta Tsakiya, a sa'i daya kuma, ya bukaci bangarori daban daban da su samar da dama mai kyau don kare fararen hula, tare da kiyaye zaman lafiya da farfado da oda a kasar.(Bako)