in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan kungiyar Kodibuwa
2013-01-31 14:16:26 cri
A gasar cin kofin Afirka ta bana dake gudana yanzu haka a Afirka ta kudu, kungiyar Cote d'Ivoire ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin yiwuwar zasu iya lashe kofin a bana.

Ganin kungiyar ta riga ta shiga zagayen wasa na dab da kusa da na karshe, ya sa ake kallonta a matsayin kungiyar da ake sa ran ganin ta taka rawar gani a karshen gasar ta bana, don haka, kamata ya yi, mu sa lura kan wannan kungiya, inda za mu bayyana cocinta da kwararrun 'yan wasan da take da su.

Kungiyar Cote d'Ivoire a tarihinta ta taba shiga zagayen kashen gasar cin kofin Afirka har karo 19, ta kuma taba lashe kofi a shekarar 1992, da samun matsayi na biyu a shekarar 2006 da 2012. Yanzu haka kungiyar na matsayi na 14 a jadawalin kwararrun kungiyoyin kwallon kafa na duniya da hukumar FIFA ta fitar a watan Janairun bana.

Cocin kungiyar Cote d'Iviore Sabri Lamouchi da a baya bai taba zama coci ga wata kungiya ba, ya ba mutane mamaki, ganin irin rawar da ya taka, tun lokacin da kungiyar ta ba shi damar zama cocinta a watan Mayun shekarar bara, bayan ta sallami cocinta na da Francis Zahoui, wanda ya jagoranci kungiyar shiga zagayen karshe na gasar cin kofin Afirka a karon da ya gabata. Bayan da sabon cocin, wato Sabri Lamouchi ya fara aiki, kungiyar Cote d'Ivoire ta lashe wasanni 6 da ta buga a jere. Shi ma Lamouchi dai ya taba taka leda a kasar Faransa, har ma ya taba halartar gasar cin kofin zakarun kasashen turai EURO ta shekarar 1996. Kuloblikan da ya taba halarta sun hada da AJ Auxerre, Monaco, Paris St Germain, Parna da Inter Milan.

Bayan cocin kungiyar, za mu bayyana wasu kwararrun 'yan wasan dake taka leda a kungiyar. Na farko shi ne dan wasan gabanta Didier Drogba, mai shekaru 34 a duniya, yana cikin wani kulob din kasar Sin mai suna Shanghai Shenhua. Gasar cin kofin Afirka ta bana na iya zamewa Drogba dama ta karshe, ta lashe wannan kofi tare da kulaf din kasar tasa, saboda yawan shekarun sa a yanzu.

A baya dai Drogba ya halarci gasar har sau 5, inda a gasannin 2 da suka gabata Cote d'Ivoire ta zama na 2. Ya kuma zubarwa kulaf din nasa a bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka yi a karshen wasan karshe na gasar bara, kamar yadda aka yi a gasar cin kofin Afirka da ta gudana a kasar Masar a shekarar 2006. Amma a watan Mayun bara, makin da ya samu ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida ya sa kulob din sa na da, wato Chelsea lashe gasar zakarun duniya wato Champions League.

A baya Drogba ya bugawa kungiyar Cote d'Ivoire wasanni har karo 89, inda a gaba daya ya sanya kwallaye 56 cikin raga.

Ban da Didier Drogba, za mu mai da hankali kan Yaya Toure, dan wasan tsakiya mai shekaru 29 a duniya, wanda ke buga kwallo a kulob din Manchester City na Birtaniya.

Yaya Toure ya samu lambar yabo ta fitaccen dan wasan kwallon kafa mafi kwarewa a nahiyar Afirka a shekarar 2011 da 2012. Sai dai tarihinsa na buga kwallo na da sarkakiya, ganin ya taba taka leda a kuloblikan kasashe 7 kafin kaurarsa zuwa Birtaniya, bayan gasar cin kofin duniya na shekarar 2010, inda ya taimaki kulob dinsa Manchester City wajen lashe gasar Premier League a watan Mayun bara.

Sa'an nan za mu duba dan wasan gaba na kungiyar Cote d'Ivoire Gervais Yao Kouassi, wanda aka fi san shi da sunan Gervinho. Dan wasan mai shekaru 25 a duniya, ya kasance babban tauraro a filayen wasannin kasar Faransa a shekarar 2011, inda ya jagoranci kwalob din Lille wajen lashe gasar liga na farko, don haka ya samu damar komawa zuwa kalob din Arsenal na Birtaniya. Bayan canza shekarsa ya samu karin albashi, sai dai bai samu dacewa da tsarin kungiyar sosai ba, har ma hakan ya sanya aka fara ganin kasawarsa, ga misali, ba ya son sanya kwallo da ka, ya kan zabi juya jikinsa don buga kwallo da kafa, duk da cewa sanya kan yafi sauki a wasu lokuta.

Gasar bana ta zama karo na 4 da ya shiga zagayen karshe na gasar cin kofin Afirka, kana a gasar bara ya sanya kwallo cikin raga a wasan kusa da na karshe da kungiyarsa ta buga da Mali.

Kugiyar Cote d'Ivoire ta ci gaba da kasancewa abin kaunar masu kallo a wanna karo, kamar yadda ta kasance a gasannin cin kofin Afirka 4 da suka gabata. Sai dai a ko wane karo ta kan kai daf da taba kofin, amma sai ta kasa, don haka, irin zumudin da ake dorawa wannan kungiya ka iya zame mata wata matsala da ke hana ta nuna cikakken karfi, duk da cewa a wannan karo itace mafi kwararrun 'yan wasa idan an kwatanta ta da sauran kungiyoyin da suka halarci gasar cin kofin Afirka ta bana.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China