A karon farko, kasar Sin ta tura 'yan sandan kwantar da tarzoma na musamman zuwa kasar Laberia, domin shiga aikin wanzar da zaman lafiya na MDD.
A cewar ma'aikatar tsaron al'ummar kasar ta Sin, rundunar wadda ta bar birnin Beijing ranar Litinin 21 ga wata, ta kunshi 'yan sanda 140, wadanda aka zabo daga rundunar lardin Heilongjiang, suka kuma samu nasara a jarabawar da MDD ke shiryawa masu aikin wanzar da zaman lafiya, bayan horo na watanni uku.
Daga shekarar 2000 da ta gabata zuwa yanzu, kasar Sin ta tura jami'an 'yan sanda 1,946 ayyukan wanzar da zaman lafiya daban daban, karkashin tawagogin MDD. (Saminu)