Jam'iyyun siyasa 28 da suka daddale yarjejeniyar farko ta wucin gadi domin fitar da kasar Guinee-Bissau daga rikicin siyasa, sun bayyana cewa, ba su amince ba da yarjejeniyar da aka cimma a kwanan nan tsakanin PAIGC da PRS, manyan jam'iyyu biyu na kasar. A cikin wata sanarwa, gungun jam'iyyun siyasar ya zargi jam'iyyar PAIGC mai 'yan majalisa 67 cikin 100 da jam'iyyar PRS mai 'yan majalisa 28 da rashin girmama yarjejeniyar siyasa da suka daddale tare da su, kungiyoyin fararen hula da shugabannin sojoji, da kuma yin Allah wadai da lalata akidar wannan yarjejeniya. Har ila yau, gungun ya nuna shakkunsa kan rashin ganin wakilin kungiyar ECOWAS a yayin daddale wannan yarjejeniya tsakanin PAIGC da PRS, tare da jaddada cewa, taimakon kungiyar yammacin Afrika na da muhimmanci sosai a wannan lokaci na tabbatar da tsarin demokaradiyya a kasar Guinee-Bissau.
A karkashin jagorancin kungiyar AU da MDD, jam'iyyun PAIGC da PRS sun cimma wannan yarjejeniya a kwanan nan domin ba da kwarin gwiwa ga zagaye na biyu na wucin gadi da zai taimaka wajen fitar da kasar daga rikicin siyasar da take fama da shi tun bayan juyin mulkin ranar 12 ga watan Afrilun shekarar 2012. A cikin manyan batutuwan da jam'iyyun biyu suka cimma, akwai maganar rike faraministan kasar, Rui Duarte Barros kan mukaminsa, wa'adin mulkin wucin gadi ba zai wuce watan Disamban shekarar 2013 ba, da kuma kafa dandalin sasanta 'yan kasa da shawarwari tsakanin jam'iyyun siyasa domin aiwatar da yarjejeniyar shirya zabubuka. (Maman Ada)