in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Isra'ila ya ya kiran da a hanzarta soke yarjejeniyar hadin kai tsakanin Fatah da Hamas
2011-05-04 14:36:37 cri

Ranar Talata Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bukaci shugaban hukumar ikon kan alummar Palasdinu Mahmud Abbas da ya sake duba shawarar da aka yanke a makon da ya gabata na sasantawa da Hamas cikin gwamnatin hadin kan kasa.

Yayin da lokaci ke kurewa a shirin sanya hannun da aka yi a birnin Alkhahira ranar Laraba, Netanyahu ya yi kira ga Abbas da ya hanzarta soke gwamnatin kana ya zabi turbar zaman lafiya da Isra'ila.

Kiran firaministan ya zo a dai-dai lokacin da ya ke ganawa da Quartet manzon Tony Blair a birnin Kudus, Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Abu Mazen(Abbas) da Hamas ta kawo karan tsaye ga shirin wanzar da zaman lafiya.

Netanyahu yana shirin kai ziyara Paris da Burtaniya a ranar Talata, a kokarin shawo kan kasashen biyu da su amince da matsayin kasar Isra'ila wajen kafa kasar Palasdinu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China