Aliko Dangote yana da shekaru 56 da haihuwa, kuma ya kafa kamfaninsa mai suna "Dangote Group" a birnin Lagos dake kasar Nijeriya a lokacin da yake da shekaru 23. A shekarar 1999, Dangote ya kai ziyara a kasar Brazil, inda ya samu wani sabon tunani daga bunkasuwar sha'anin kera kayayyaki a kasar Brazil. Domin yawancin kayayyakin da ake saya a kasar Nijeriya suna fitowa ne daga kasashen waje, Dangote ya fara gudanar da harkokinsa da cinikayya a fannonin samar da siminti, hoda, sukari, gishiri da kuma shayi da abinci. A halin yanzu kuma, harkokinsa na shafar mashigin teku, gidaje, sadarwa, man fetur, iskar gas, karfe da dai sauransu, kuma ana amfani da simintinsa a dukkan nahiyar Afirka. (Zainab)