in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babbar ganuwa
2013-10-25 19:34:42 cri

Danladi: Ko shakka babu haka ne abin da ka fadi malam Maman Ada, Kuma an gina babbar ganuwa ne da manyan tubala da duwatsu da aka hada da kasa da buraguzan duwatsu, sannan tsayinta ya kai mita 10 yayin da fadinta ya kai mita biyar wato dawaki 5 suna iyar tafiya a kanta gaba daya dauke da abinci da makamai. A kan hau bisa ganuwa ta matattakara sannan akwai dakalin kunna wuta domin sojoji masu sintiri su kunna wuta da zaran sun hango makiya domin sanar da mutane.

Maman: Lalle a zamin da gina babbar ganuwa ya kawo babban tasiri ga tsaron kasar Sin da jama'arta ganin yadda wannan ganuwa ta taimaka wajen kare daulolin kasar Sin daga hare hare da yake yake da kuma taimakawa cigaban kasar. To malam Danladi a yanzu ina matsayin wannan ganuwa a wannan zamani da muke ciki musammun ga kasar Sin da ma duniya baki daya?

Danladi: A zamanin yau, malamMaman Ada, babbar ganuwa bata aikin tsaro amma yanzu ta zama wani muhimmin wuri na kai ziyara ga masu yawon bude ido na kasar Sin da na kasashen duniya. Mutane su kan nuna mamaki sosai kan irin wannan gini mai kayatarwa na mutanen dauri domin babbar ganuwa musammun ma girmanta da tsayinta suna jan hankalin mazu ziyarar wannan wuri. A kan ce idan aka hango babbar ganuwa ta sararin samaniya dake kan tsaunuka za'a ce ta yi kama da wani babban dodo. Babbar ganuwa ta nada babbar daraja a idon masu yawon shakatawa domin tana shaida al'adun tarihi na kasar Sin. A kasar Sin, sinawa kan ce, zuwa babbar ganuwa tare da hawanta sai jarumi. Masu ziyarar yawon shakatawa da shugabannin kasashen waje da suka zo kasar Sin su kan yi alfahari saboda sun hau babbar ganuwa.

Maman: Ina ganin ya dace malamDanladi mu bayyana cewa a kan samu babbar ganuwa a wasu yankunan kasar Sin kamar yadda muka ambata a farkon wannan shiri domin haka maganar take. A yanzu haka akwai wasu sassan babbar ganuwa da aka kiyaye da kyau misalin babbar ganuwa ta Badalin, Simatai da Mitianyu na Beijing sannan kuma a ganiyar gabas ta babbar ganuwa akwai babbar kofa ta farko ta kasar Sin wato Shanhaiguan, yayin da a ganiyar yamma ta babbar ganuwa akwai Jiayuguan na lardin Gansu. Duk wadannan wurare dana zayyana sun shahara sosai wajen yawon bude ido a kasar Sin.

Danladi: Haka ne kuma babbar ganuwa ta kasar Sin na bayyana hikima da kokarin da jama'ar kasar Sin suka nuna a zamanin da wajen gina wannan abin al'ajabi bayan shekaru dubbai da suka gabata, kuma har yanzu tana tsaye kuma zata cigaba da tsayawa tsaye a kasar Sin domin ta riga ta zama alamar ruhu nal'ummarkasar Sin. To malam Maman Ada ko akwai irin wannan ganuwa a wasu kasashen duniya musammun ma a nahiyarAfrika?

Maman: Hakika Danladi tarihi ya nuna cewa akwai kasashen dama a yankin turai, asiya da ma nahiyar Afrika inda aka lokacin dauloli musammun a zamanin wasu sarakuna suka yi tunanin gina ganuwa ko katanga domin kare kasarsu da jama'arsu daga hare hare da yake yake, kamu a wasu kasashen har yanzu ana iyar ganin shaidar ganuwa kamar a jihar Kano ta tarayyar Najeriya, a wasu yankunan birnin Paris na kasar Faransa da sauransu…

Danladi: To masu sauraro ina ganin da haka za mu dasa aya a cikin shirin mu na Allah daya gari bamban inda a yau tare da abokin aikina Maman Ada kuma tattauna kan babbar ganuwa ta kasar Sin da fatan kun ji dadin wannan shiri. Ni ne Danladi daga nan sashen hausa na rediyon kasar Sin CRI nake cewa sai kuma wani mako mai zuwa idan Allah ya kai mu ku huta lafiya.


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China